Illustration of a Photojournalist, Frontline Rescuer, and Aid Worker in a war zone

War Toys: Evac Ops™ wani abin wasan haɗaka ne na ƴanwasa uku: Mai Ceto, Mai Ɗauƙar Hoto A Fagen Daga, Da Ma’aikacin Agaji. Dole ne ku yi aiki tare kuma ku yi amfani da ƙwarewa ta musamman don ceton ƴanwasa a yanki mai haɗari. Yi aiki da sauri kafin lokaci ya ƙare, ƴanwasa, ko nasara!

  • Fronline Rescuers

    Aikin Mai Ceto shi ne kuɓutar da mutanen da zai iya daga wurare ma su hatsari. Su na da horo na musamman da ƙwarewa kan ceton mutane bayan fashewr bom ɗin da aka kai hari ta sama, ko manyan makamai, ko bom na mota.

  • Combat Photojournalists

    Mai Ɗaukar Hoton filin daga shi ne ya ke tattara abubuwan da ke faruwa a wurin yaƙin tare da yaɗa bayanai ga ragowar mutane. Hotunansu na taimakawa Mai Aikin Agaji da Mai Ceto samun kulawa ga aikinsu su samu kayan aiki.

  • Aid Workers

    Mai taimako na kuɓutar da ƴanwasa sannan kuma ya na samar mu su da mafaka. Yawanci su na aiki ne da ƙungiyoyin jin ƙai. Kuma su na yin ayyuka iri-iri da su ka haɗa da bayar da kulawar lafiya, samar da sansanin ƴan gudun hijira, da kuma kawo abinci da sauran kayan buƙata.

Illustration of player sharing a mobile device to play a board game

Evac Ops ya fi daɗi idan an zauna kusa da allon wasa, kuma ana iya buga shi ta hanyoyi da dama:

  1. Ku na iya raba wannan na'urar ta wayar hannu tsakanin ƴanwasa kuma a bar manhajar Evac Ops ya jagorance ku a duk lokaci da kowannen ku ke bugawa.

  2. Ku na iya bin umarnin da ke ƙasa don yin amfani da kayan wasan da aka haɗa tare da wasu kayayyakin wasan.

  3. Ko kuma a ziyarci shafin yanar gizon EvacOps.app don saukewa da buga naku kayan wasan.

Prototype of War Toys: Evac Ops board game

Evac Ops Kayan Wasa

Khaled

Mouna

Dominique

Ashok

Asmaa

Byron

Ron

Vero

David

Chris

Nicole

Dickey

Ma fi yawan kayan wasannin sun haɗa da: 2x Masu ceto guda biyu, 2x Ma’aikatan Agaji biyu, da 2x Mai ɗaukar hoton fagen daga (ba a jere ba)

Ƙungiyar sa-kai ta War Toys® ce ta ƙirƙiri Evac Ops™ tare da tallafin:

Wanda suka ƙera:
Believe-Fly Toys Co., Ltd. Shantou, China
Jimillar Tambayoyi (MOQ 3000 pcs):
market@beflytoys.com