War Toys: Evac Ops™
Ka’idodin Tsare Sirri

Wannan Ka’idodin Tsare Sirri ya shafi War Toys: Manhajar Evac Ops™ (wanda ake kira "Manhaja") na na'urorin hannu waɗanda War Toys® su ka ƙirƙira (wanda ake kira "Mai ba da Tsarin") a matsayin kyauta. Wannan tsarin an yi ne don amfani da shi "KAMAR YADDA YA KE".

Waɗanne bayanai ne manhajar ke samu kuma ta yaya ake amfani da su?
Manhajar ba ta karɓar wani bayani lokacin da ka sauke kuma ka yi amfani da shi. Ba a buƙatar yin rajista don amfani da Manhajar.

Shin Manhajar na tattara takamaiman bayanan wurin na'urar kai tsaye?
Wannan Manhajar ba ta tattara takamaiman bayanai game da na'urarka ta hannu.

Shin wasu daban na iya gani da / ko samun damar samun bayanan da aka samu ta hanyar Manhajar?
Tun da Manhajar ba ta tattara kowane bayani, babu bayanan da aka bayar ga wasu.

Mene ne haƙƙin na?
Za ka iya dakatar da duk tarin bayanai da Manhajar ke karba cikin sauƙi ta hanyar cire shi. Ku na iya amfani da daidaitattun hanyoyin cirewa kamar yadda za a iya samu a matsayin wani ɓangare na na'urarka ta hannu ko ta hanyar shafin manhajar wayar ko cibiyar sadarwa.

Yara

Ba a amfani da Manhajar don neman bayanai da gangan daga ko tallatawa ga yara ƴan ƙasa da shekaru 13.

Mai ba da tsarin ba ya tattara bayanan sirri da gangan daga yara. Mai ba da tsarin na ƙarfafa duk yara da kada su taɓa gabatar da kowane bayanan sirri ta Manhajar da / ko Tsare-tsaren. Mai ba da tsarin na ƙarfafa iyaye da ma su kula da yara don saka idanu kan amfani da yanar gizo na yaransu kuma su taimaka wajen aiwatar da wannan Ka’idodin ta hanyar umartar 'ya'yansu da kada su taɓa bada bayanan sirri ta Manhajar da / ko Tsare-tsaren ba tare da izinin su ba. Idan ku na da dalilin da za ku yi amanna cewa yaro ya ba da bayanan sirri ga Mai ba da Tsarin ta hanyar Manhajar da / ko Tsare-tsaren, a taimaka a tuntuɓi Mai ba da Tsarin (info@wartoys.org) don su sami damar ɗaukar matakan da su ka dace. Har ila yau, dole ne ku kasance aƙalla shekaru 16 don yarda da aiwatar da bayananku na sirri a cikin ƙasarku (a wasu ƙasashe za mu iya ba da izinin iyayenku ko mai kula da ku don yin haka a madadinku).

Tsaro

Mai ba da tsarin ya na damuwa game da kiyaye sirrin bayananku. Duk da haka, tun da Manhajar ba ta tattara kowane bayani, babu haɗarin samun damar bayananka ta hanyar mutane marasa izini.

Canje-canje

Ana iya sabunta wannan Ƙa’idodin Tsare Sirri daga lokaci zuwa lokaci don kowane dalili. Mai ba da Tsarin zai sanar da ku game da duk wani canje-canje ga Ka’idodin Tsare Sirri ta hanyar sabunta wannan shafin tare da sabbin Ka’idodin Tsare Sirri. An shawarce ku da ku duba wannan Ka’idodin Tsare Sirri akai-akai don kowane canje-canje, don ci gaba da amfani ana ɗaukarsa amincewa da duk canje-canje.

Wannan Ka’idodin Tsare Sirri na aiki daga 2024-05-01

Amincewar Ku

Ta amfani da Manhajar, ku na amincewa da a yi amfani da bayananku kamar yadda aka tsara a cikin wannan Ka’idodin Tsare Sirri yanzu kuma kamar yadda Mai Ba da Tsarin ya shirya.

Tuntuɓe Mu

Idan ku na da wasu tambayoyi game da tsare sirri yayin amfani da Manhajar, ko tambayoyi game da ayyukan, da fatan za a tuntuɓi Mai ba da Tsarin ta hanyar https://wartoys.org/contact.